Kasuwanci
Ma’aikatan AEDC sun yi barazanar tsunduma yajin aiki

Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Birnin tarayya Abuja AEDC, sun yi barazanar tsunduma yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja da Kogi da Nasarawa da Jihar Neja cikin halin duhu.
Ta cikin sanarwar da Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, suka fitar a baya baya nan sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024.
Ma’aikatan Kamfanin sun ce sun yarda su dakatar da yajin aiki a watan Nuwamban 2024 saboda alƙawuran da kamfanin ya ɗauka, amma har yanzu ba a aiwatar da su ba a cewar jagoran ƙungiyar, Opaluwa Eleojo Simeon.
Daga cikin Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata.
Sai ƙin biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka
You must be logged in to post a comment Login