Labarai
Mahaddatan alƙur’ani sun goyi bayan Ganduje kan hana bara
Ƙungiyar mahaddatan alƙur’ani ta ƙasa ta ce za ta tabbatar da hana barace-barace a tsakanin almajirai.
Shugaban ƙungiyar Gwani Aliyu Salihu Turaki ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da suka kai wa gwamnan Kano.
Gwani Aliyu ya ce, za su tsaya kai da fata wajen tabbatar da ƙara inganta makarantun tsangayu a Kano.
Labarai masu alaka:
Dalilan da suka sanya Ganduje ya hana bara a Kano – Dr. Sa’idu Dukawa
Ganduje zai fara kwashe almajirai dake barace-barace akan tituna
Shi kuwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje cewa ya yi, gwamnatinsa ba ta da burin hana karatun tsangaya.
Hassalima tana da shirye-shirye na musamman domin ƙara inganta tsarin karatun.
Gwamna Ganduje ya ce, gwamnatinsa za ta ƙara jajircewa wajen ganin an daƙile bara domin tana haifar da illa ga almajirai.
Ku kalli hotunan ziyarar da kungiyar ta kai wa gwamnan
You must be logged in to post a comment Login