Manyan Labarai
Mahangar masana kan baiwa shugabannin majalisu kariya
A baya-bayan nan ne kudurin dokar da ke neman gyara sashe na 308 na kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999, wanda zai baiwa shugabannin majalisun dokokin tarayya kariya a lokacin da suke kan mulki, ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.
Tun farko dai Dan majalisa Odebumi Olusegun daga jam’iyyar APC daga jihar Oyo ne ya gabatar da kudirin a yayin zaman majalisar a makon da ya gabata.
Kundirin dai ya janyo cece-cece kuce tare da fuskantar tirjiya daga al’ummar kasar nan wadanda wasu ke ganin hakan wata dabara ce ta neman kaucewa fuskantar shari’a a lokacin da suke mulki.
Sai dai a cewar dan majalisa Odebumi Olusegun, kudurin zai kuma bai wa shugabannin majalisun jihohi kariya, kamar yadda gwamnoni da mataimakansu ke da shi, wanda hakan zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
Wakilin Freedom Rediyo Umar Idris Shuaibu ya tattauna da masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero da ke nan Kano, Farfesa Kamilu Sani Fagge, inda ya ce wannan kuduri ya ci karo da ayyukan da ya kamata ‘yan majalisun su maida hankali a kai, da suka shafi ciyar da al’umma gaba a fannonin rayuwa.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya kara da cewa, shakka babu matakin ba a abin da zai haifarwa kasar nan, sai koma baya a tsarin mulkin Dimukuradiyya.
Masanin kimiyyar siyasar dake Jami’ar Bayero ta Kano, ya kara da cewar ganin matsalolin da suka dabaibaye al’umma a wannan lokaci, bai kyautu mahukuntan su dage wajen aiwatar da irin wadannan dokoki ba, da idan ka kalle su ba abin da za su yiwa talakawan su da suke wakilta da ya wuce kara jefa su cikin matsalolin rayuwa na yau da kullum.
Shi kuwa wani masanin shari’a Barrister Salisu Aliyu Muhammad, ya yi fashin baki kan kudurin dokar, inda ya ce tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 ya basu ikon sauya kowace irin doka.
Masanin shari’ar ya Kara da cewa, hakan kuwa zai yiwu ne idan har suka samu biyu bisa uku na mambobin majalisun kasa, da kuma kwatankwacin hakan a majalisun jihohin kasar nan 36, sannan za su iya yin kowane irin sauyi.
Masana tsarin mulkin kasa dai na cewa, shakka babu tabbatar da tsarin bai wa shugabannin majalisa kariya, ka iya zama wata dama da za ta sanya su shagalta daga manufofi na ciyar da kasa gaba.
You must be logged in to post a comment Login