Labaran Kano
Mahukunta sun rufe makarantar KCC Kano
Daliban makarantar Aminu Kano Commercial College dake nan Kano, sun gudanar da wata zanga-zanga da safiyar yau, sakamakon zargin da suka yin a cewa ana kokarin kwashe musu malaman makarantar wanda su kuma basu gamsu da hakan ba.
Wasu daliban makarantar da suka zanta da wakilin mu Mu’azu Musa Ibrahim sun bayyana cewa sun zo makaranta amma jami’an ‘yan sanda sun hana su shiga makarantar wanda hakan bai yi musu dadi ba, akan hakan ne kuma suka shirya zanga-zangar lumana, sai dai sun fuskanci martani daga jami’an tsaro da suka tarwatsa su.
Har ila yau daliban sun tabbatar da cewa sun daki wani malami daga cikin malaman makarantar a yayin wannan al’amari.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar mana da cewa jami’an su sunje wurin sun kuma kasha tarzomar da daliban suka so kunnawa, kuma tuni hukumar makarantar ta rufe makarantar har sai bayan sati biyu.
Duk wani yunkuri da mukayi na jin ta bakin hukumar dake lura da makarantun sakandire ta jihar Kano abin yaci tura.
RUBUTU MASU ALAKA:
Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood cikin makon da ya gabata
Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa
Ko mene ne makomar ‘yan marin da ake sakowa?
Fitar Zaki a Kano: Akwai bukatar duba na tsanaki kan gidan adana dabbobin daji