Labarai
Sarkin Daura yace Oshinbajo na da biyayya
Mai martaba sarkin Daura yace Oshinbajo na da biyayya
Mai martaba sarkin Daura Alhaji Faruq Umar ya yabawa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo saboda biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa.
Rahotannin sun bayyana cewar mataimakin shugabn kasa Farfesa Yemi Oinbajo ya je garin Daura ne don bikin nadin Musa Haro wanda da ne a gun shugaban kasa Muhammadu Buhari.
An dai nada Alhaji Musa Haro a matsayin Danmadamin Daura wanda tana cikin saurata mafi girma a cikin masarautar Daura.
Sarkin Daura Alhaji Faruq Umar ya sake bayyana Osinbajo a matsayin amintace mai rikon gaskiya da Amana wanda yake da kishin Najeriya a cikin zuciyar sa.
Sarkin na Daura yace masarautar Daura zata cigaba da marawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya wajen cimma manufofin da ta sanya a gaba.
Ina yabawa ‘yan sandan jihar Kano –Magajin garin Daura
Rundunar yan sandan Kano ta kubutar da Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar
Masarautar Daura ta bayyana cewar an nada Alhaji Musa Haro a matsayin Danmadamin Daura ne saboda gudunmawar da yake bai masarautar Daura da ma jihar Katsina baki daya.