Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisa ta amincewa Ganduje ya ciwo bashi

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amincewa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya ciwo bashin naira Biliyon Hamsin domin gudanar da ayyukan raya kasa a fadin jihar ta Kano.

Hakan ya biyo bayan karanta wasika da aka yi a zauren majalisar yau wacce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aiko.

Bukatar da gwamna Ganduje ya turawa majalisar ta nemi a amince da bashin na Biliyan Hamsin domin gudanar da ayyuka na raya kasa sakamakon alkawarurruka da gwamnati ta dauka lokacin yakin neman zabe na shekarar bara.

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da manbobin ta guda 5

Majalisar zartarwa ta Kano ta shiga taron gaggawa

Wakilin mu na majalisar dokokin jihar Kano Auwal Hassan Fagge ya rawaito cewa bashin naira Biliyan Hamsin din da majalisar ta amince da shi za’a biya a shekaru goma masu zuwa.

Daga nan majalisar ta dage zamanta zuwa 13 ga watan gobe na Afrilu sakamakon ballewar cutar Corona a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!