Labarai
Majalisar dattijai ta zayyano wasu matsalolin da ke gabanta
Majalisar Dattijai ta zayyano wasu matsaloli da ke gabanta, da suka zamo karfen kafa wajen amincewa da kudurin samar da ‘yan-sandan Jihohi a kasar nan.
Shugaban Kwamitin harokin ‘yan-sanda na Majalisar Sanata Abu Ibrahim ne ya shaida hakan yana mai cewa matukar aka gaza warware su to shakka babu zai yi wuya a iya sahalewa kudurin har ya zama doka.
Abu Ibrahim Ibrahim ya ce matsalolin sun hadar da gazawar gwamnoni wajen samar kudaden gudanarwar ‘yan-sandan Jihohin, da kuma zargin yadda gwamnonin za su iya mayar da ‘yan-sandan karnukan farautarsu.
Sai kuma batun rashin cimma matsaya guda tsakanin wasu ‘ya’yan Majalisar da gwamnoninsu sakamakon rashin fahimtar da ke tsakaninsu.
Ya kara da cewa akwai bukatar yin kwaskwarima kan tsarin rabon arzikin kasa domin baiwa Jihohi kaso mai tsoka, a matsayin wani tsani na basu damar kula da ‘yan-sandan na su.
Haka zalika Majalisar ta gano cewa Jihohi kalilan ne za su iya daukar gabaren kula da ‘yan-sandan Jihohin, wadanda suka hadar da Lagos da Rivers da Akwa Ibom da Kano sai watakil Kaduna.