Labaran Kano
Majalisar dokokin Kano ta dakatar da manbobin ta guda 5
Majaisar dokokin jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta guda biyar sakamakon zarginsu da tada hatsaniya a makon jiya.
A cewar majalisar dakatarwa wadda ta fara aiki nan ta ke, za ta kwashe tsawon watanni shida tana gudana.
Shugaban majalisar dokokin jihar ta Kano Abdul’aziz Garba Gafasa shi ya sanar da dakatar da ‘yan majalisar yayin zaman majalisar na yau.
Ya ce wadanda majalisar ta dakatar sun hada da,Alhaji Garba Ya’u Gwarmai mai wakiltar karamar hukumar Kunchi da Tsanyawa da Abdul Labaran Madari wakilin mutanen Warawa da Muhammed Bello Butu-Butu mai wakiltar karamar hukumar Tofa da Rimin-Gado.
Majalisar zartarwa ta Kano ta shiga taron gaggawa
A yau ne majalisar dattijai zata tabbatar sunayen ministoci bayan tantance su
Mutanen Ja’en za su yi karar majalisar dokokin Kano
Sauran sune, tsohon shugaban majalisar, Isyaku Ali Danja mai wakiltar karamar hukumar Gezawa da kuma Salisu Maje Ahmed Gwangwazo wakilin birni da kewaye Kano.
You must be logged in to post a comment Login