Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An shawarci dalibai su zamanto masu dogaro da kansu da sana’oi

Published

on

Kungiyar dalibai musulmai ta kasa reshen jihar Kano ta shawarci al’ummar musulmai dasu kasance masu ruko da sana’oin dogaro da kai a maimakon yawan dogara neman aikin Gwamnati.

Kakakin kungiyar  reshen jihar Kano Sulaiman Umar Waziri,  ne ya bayyana hakan lokacin taron walima, da karawa juna sa ni da taimakon juna  da kungiyar ta saba yi shekara.

Labarai masu alaka.

BUK: dalibai 300 sun sami tallafin karatu

Kungiyar dalibai NAKSS ta nada sabbin shugabanni

Sulaiman Umar , ya ce zuwa yanzu  ya zama wajibi al’ummar musulmai dalibai su tashi tsaye haikan wajen neman Ilimin Addini dana zamani don kuwa ta hakane za’a samu ingantacciyar tarbiyya da samun  madogara da zasu tsaya da kafafun su.

Wakilin mu da ya halarci taron  Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa, ya ruwaito cewa mambobin kungiyar da dama ne suka halarci taron wanda  aka karkare da  karrama wasu daga cikin mambobin kungiyar, sakamakon aiyyuakan da suka gudanar na bunkasa al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!