Labarai
Majiyyanta sun roki gwamnati data mayar da wankin koda kyauta a Kano
Wasu majiyyata ciwon koda a asibitin Koyarwa na Aminu, sunyi kira ga gwabnatin jihar Kano data duba yuwuwar yin aikin ciwon koda kyauta duba da kasancewar cutar mai saurin talauta al’umma ce.
Wakilin mu Aminu Audu Baka noma ne ya tattauna da wadannan majiyyata da ke cikin asibitin aminon ya kuma bayyana tattaunawar kamar haka.
Wani majinyaci dake jiyya asibitin na Aminu Kano yace saboda yanda cutar take cin kudi yasa har sai da ya sayar da gonar gadonsu guda biyu don ganin samun sauki daga cutar.
Akwai bukakatar samar da tsarin bada lafiya mai nagarta ga marasa lafiya-hukumar asibitoci
Jihar Jigawa ta yi wa Kano fintinkau a taimakawa marasa karfi
Abubuwan da ya kamata ku sani gami da lafiyar Idanu
Haka zalika wani majiyyaci ya bayyana cewa wannan shine karo na goma sha biyu da akeyi masa aikin gashin koda, wanda yakan kashe naira dubu goma sha bakwai da naira dari a duk lokacin da za’a yi masa aikin.
Mjiyyacin ya kuma mika rokonsa ga gwamnatin jahar Kano data karo injinan gashin koda, wadanda zasu wadata a asibitin kasancewar inji guda daya ne tak a ake amfani da shi asibitin.