Labarai
Makabartar mu ta cika gwamati ta kawo mana dauki – Al’ummar Hotoro
Jama’ar unguwar Hotoro NNPC, sun koka tare da bukatar gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu dauki domin gyara Makarbar yankin wacce ta cika a halin yanzu.
A cewarsu a yanzu haka ba sa da inda za su binne gawarwaki in anyi mutuwa a unguwar sakamakon cikewa da makabartar ta yi.
Shugaban kwamitin ci gaban unguwar ta Hotoro NNPC Malam Garba Hussein Isyaku ne ya yi wannan kiran yayin gangamin aikin gyara makabartar da suka gudanar da safiyar yau Asabar.
Ya ce, a baya al’ummar yankin sun yi bakin kokarin su , inda gwamnatin jiha tayi musu alkawarin basu fili, amma kawo yanzu lamarin ya ci tura.
Wasu daga cikin dattijan yankin, sun yi karin bayani dangane da yadda lamarin makabartar yake a halin yanzu, inda suka ce sun dade suna bibiyar gwamnatin don ganin ta saya musu filayen da ke makwabtaka da makabartar don a fadada ta.
Wakilinmu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito cewa al’ummar yankin , sun bukaci gwamnati da masu hannu da shuni da su shigo cikin lamarin don taimaka musu
You must be logged in to post a comment Login