Manyan Labarai
Malaman jami’a da basu yi Rijistar IPPIS ba, kada su sa ran karbar albashi.
Gwamnatin tarayya ta ce mambobin kungiyar manyan malamn jami’a ta kasa ASUU da suka ki yin biyayya ga shiga tsarin Gwamnatin na IPPIS kada su tsammacin samun albashin su.
Ministar kudi ta tarayya Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan da yammacin jiya Alhamis lokacin da ake bikin bude taron karawa juna sani na bana wanda aka shiryawa manyan jami’an kula da harkokin kudi da binciken su na ma’aikatar a nan Kano.
Hajiya Zainab ta kuma ce kaso 55 na malam jami’ar basu yi rajistar da tsarin ba tana mai karin bayanin cewa daga lokacin da aka bijiro da tsarin an samu damar bankado ma’aikatan bogi fiye da dubu 70.
Labarai masu alaka.
Ba za mu shiga tsarin IPPIS ba -ASUU
Tsarin albashi na IPPIS: Kungiyar Malaman Jamioi na Jayayya da Gwamnatin tarayya.
Ta ce Gwamnatin tarayya ta bijiro da tsarin na IPPIS ne don tabbatar da cewa halastattun ma’aikatan gwamnati ne kadai ke karbar albashi ba wai na bogi ba.
Daga nan kuma sai ta yabawa Gwamnatin tarayya kan yadda ta ke bijirowa da tsare-tsare manaragta don inganta tsarin aikin gwamnati, tana mai cewa hakan na rage ha’inci da sn zuciya a yayin tafiyar da aikin gwamnati a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login