Connect with us

Labaran Wasanni

Manchester City ta lashe gasar firimiyar ƙasar Ingila

Published

on

Manchester City ta lashe gasar firimiyar ƙasar Ingila bayan da ta samu nasara a kan Aston Villa da ci 3-2 a wasan ƙarshe na gasar.

Manchester City ta ɗauki gasar ta shekarar 2021/2022 a yau Lahadi 22/5/2022, bayan buga wasanni 38 na gasar.

Tun a mintuna na 37 ƙungiyar Aston Villa ta shiga gaban Manchester City bayan da ɗan wasan ta Matty Cash ya zura ƙwallon farko, sai kuma a mintuna na 69 ɗan wasa Philip Coutinho ya ƙara ƙwallo a ragar Manchester City wanda ya zama jimilla suna da ƙwallo 2.

Sai dai a minti na 76 likay Gundigon na Manchester City ya warware ƙwallon farko kafin daga bisani a mintuna na 78 ɗan wasa Rodry ya warware ƙwallayen 2 da Aston Villa ta zura musu.

A minti na 81 ɗan wasa Likay Gundigon ya ƙarawa ƙungiyar sa ta Manchester City ƙwallo wanda ya zama jimilla Manchester City tana da ƙwallo 3 ita kuma Aston Villa tana da 2.

Kuma da wannan nasara ce yasa Manchester City lashe gasar firimiyar Ingila ta shekarar 2021/2022 da maki 93.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!