Labaran Kano
Manyan abubuwa 4 da hudubar da Muhammadu Sunusi II ta kunsa
Tsohon sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na II, mai murabus ya gabatar da hudubar Jumma’a a babban masallacin garin Awe da jihar Nasarawa tare da jagorantar Sallar a yau.
Malam Muhammadu Sunusi na II, da yake tare da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i , wanda ya kai masa ziyara a safiyar yau , a gidan da aka killace tsohon sarkin dake karamar hukumar na Awe , a jihar Nassarawa tun bayan da sauke shi daga Karagar Mulki da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar litinin din makon nan.
Malam Muhammadu Sunusi na II, wanda ya dauki kusan Awa guda yana hudubar ,
- Ya yi kira ga al’umma dasu ji tsoron Allah tare da Sallama lamuran su gareshi a koda yaushe ba tare shakku ko akasin haka.
- Haka zalika daga cikin kunshin hudubar, ta kara jan hankalin mutane , da su karbi kaddara kyakyawa ko akasin ta, a duk yadda ta same su kasancewar dukkanin nasara tana tare da hakuri.
- Sarkin, ya rufe hudubar , da kiran al’umma musulmi dasu hada kansu da taimakon junan su , tare da roka musu nasara a dukkan lamuran da suka saka a gaba , cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
- Bugu da kari ya yi addu’ar zaman lafiya ga kasar nan sakamakon rikice- -rikicen da ta ke fama dasu.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan ,umarnin da wata Babbar Kotu ta bayar a Abuja, da safiyar yau na sakin Sarkin daga daurin talala da aka yi masa tare da bashi damar gudanar da rayuwar sa cikin ‘yan cin walwala ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba ko ka’idoji.
You must be logged in to post a comment Login