Labaran Wasanni
Mariri Market CUP: Yin wasanni tsakanin ‘yan kasuwa zai samar da hadin kai-Salisu Auwal
Shugaban kwamatin shirya gasar cin kofin ‘yan kasuwar Mariri da akai mata take da Mariri Cola Nut Market Cup, Salisu Auwal da akafi sani da Salisu Alaye, ya ce sun shirya gasar ne domin kara samar da hadin kai tsakanin ‘yan kasuwar.
Salisu Auwal ya ce duba da muhimmmancin da wasanni ke da shi musamman a tsakinin matasa shi yasa sukaga da cewar amfani dashi wajen sada zuminci da hadin kai a tsakin su.
Ya kuma ce nan gaba za su shirya wasan kwallon kafa tsakanin ‘yan kasuwannin jihar Kano domin samar da nishadi da hadin kai a tsakanin su.
Ahmad Musa zai iya yiwa Najeriya wasanni 140-Vincent Enyeama
A jiya Juma’a 17 ga watan Satumbar shekarar 2021 ne aka fara gudanar da gasar, inda aka buga wasa tsakin Layin Sunusi Dan Mande da Layin ‘Yan Bage, inda aka tashi wasan layin Sunusi Dan Mande na da ci 1 ya yin da Layin ‘Yan Bage ke nema.
Za’a ci gaba da wasan a ranar Lahadi 19 ga watan na Satumba tsakanin layin Bashir Roja da fc kwata da misalin karfe 5 na ranar.
Kungiyoyi 8 ne dai za su fafata a gasar inda za’a kwashe kusan watanni 2 ana buga ta.
You must be logged in to post a comment Login