Labaran Kano
Masarautar Kano ta yabawa shirin ECOWAS 2020
Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yaba wa shirin muradan raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta yamma na ECOWAS – Vision 2020 zuwa 2050.
Sarkin ya bayyana hakan ne ta bakin Ɗan Malikin Kano Ambasada Ahmed Umar, yayin taron bita da tuntuɓar juna na kwanaki biyu game da shirin, wanda aka gabatar a ranakun jiya Litinin da yau Talata a nan Kano.
Taron dai ya mayar da hankali ne kan sabbin shirye-shiryen da za a samar a shiri na gaba mai taken Vision – 2050.
Bayan kammala taron wakiliyarmu Hassana Salisu Abubakar ta tuntuɓi Ɗan Malikin Kano, wanda ya yi mana ƙarin haske game da yadda taron ya kasance.
Ɗan Malikin na Kano, ya ce, Maimartaba Sarkin Kano ya hori masu shirya shirin da su yi la’akari da jihar Kano duba da yawan albarkatu musamman na kasuwanci da jihar ke da shi.
Haka kuma, Sarkin na Kano ya ce, la’akari da tasirin da cutar Coronavirus ta yi wajen kassara masu sana’o’i akwai buƙatar sabon shirin ya bada fifiko wajen farfaɗo da tattalin arziƙin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login