Addini
Matakai 4 don yaki da Coronavirus a musulunce – Sheikh Daurawa
Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu matakai hudu matsayin, hanyoyi kaifiyyan da za a bi kan annobar Coronavirus.
Malam Daurawa yayi wannan jawabi ne cikin hudubarsa ta yau jumu’a a masallacin sa dake unguwar Fagge Plaza.
Mataki na farko a cewar Malam Daurawa shi ne Imani da kaddara cewa abinda Allah kaddara shi ne zai faru, musulmi yayi Imani cewa mahalicci ne ke da ikon kaddara masa rayuwar sa.
Na biyu shi ne, mu yarda da hukuncin Allah na mutuwa ko rayuwa, don haka a duk sanda mutuwa ta zo sai mutum ya tafi ko da Coronavirus ko babu ita.
Mataki na uku, daukar matakan kariya, musamman abubuwan da jami’an lafiya suke ta fada, yakamata abi wadannan matakai sau da kafa.
Abu na hudu shi ne, jama’a ta kaucewa yada jita-jita, abubuwan da ake yadawa na karya game da Coronavirus sun yi yawa.
A lokacin annobar Ebola wani ya kirkiro cewa a yi wanka da gishiri, yanzu kuwa an yiwa Annabi (s.a.w) karya cewa wai wani mutum yayi mafarki ya ga manzon Allah (s.a.w) ya ce masa ya bude alkur’ani mai girma ya duba zai ga gashi, sai ya jika shi ne maganin Coronavirus.
Cikakken rahoton zai zo muku a shirin Inda Ranka na yau @9:30pm.
Karin labarai:
Covid-19: BUK ta umarci daliban dake zaune a makarantar su koma gidajen su
Ganduje : zan yi duk mai yuwa wajen hana COVID-19 shigowa Kano
You must be logged in to post a comment Login