Labarai
Matasa fiye da 10 sun mutu a Kano sakamakon shan shayi da Zakami
Al’ummar unguwar sheka da ke karamar hukumar Kumbotso na ci gaba zama cikin alhinin rashin matasan yankin da ake zargin sun kai goma sha biyu, sakamakon shan shayin zakami da suka yi yayin murnan wani bikin aure.
Malam Abdullahi Mahmud da Hajara Abdullahi na daga cikin iyayen da suka rasu ‘ya’yansu sakamakon shan zakamin, a tattaunawarsu da Freedom Radio, sun bayyana cewa an shirya wa ‘ya’yan nasu makirci ne inda aka zuba musu Zakamin suka sha ba tare da sun sani ba.
Haka kuma sun bukaci mahukunta da su tabbatar da cewa an yi wa wadanda ke da hannu a lamarin hukuncin da ya dace.
A nasa bangaren kwamandan kungiyar sintiri ta Vigilante na yankin Malam Mahmud Isa Abubakar, ya tabbatar da cewa sun samu labarin afkuwar wannan mummunan lamari.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rundinar ‘yan sandan Kano, Ya ce, rundunar na kan gudanar da bincike a kan afukar wannan lamari, kuma za ta magantu nan ba da jimawa ba.
You must be logged in to post a comment Login