Labarai
Ya kamata matasa su tashi tsaye wajen neman yanci- Gidan yanci
Shugaban sabon shirin nan na Gidan Yanci Sadiq Muhammad Mustapha, ya bayyana cewa shigo da matasa cikin harkokin da suka shafi al’umma hanya ce da za ta kawo gyara bisa matsalolin da Nijeriya ke fuskanta duba da cewa matasa su ne kashin bayan kowacce al’umma.
Sadiq Muhammad Mustapha Ya bayyana haka ne yayin taron fadakar da matasa kan hanyoyin da ya kamata su wajen kawo gyara musamman a harkokin siyasa da kuma matsalolin da suka shafi al’umma.
Zulaihat Danjuma daya daga cikin masu bada horon tace wannan shiri na gidan yanci yana zabura da matasa ta hanyar yadda ya kamata su bi domin kwatowa kansu yanci.
Ita ma Hafsat Bello Bahara da ta kasance cikin wanda aka na yiwa bitar ta bayyana cewa zasu Yi amfani da abinda suka koya ta hanyar da ya dace.
You must be logged in to post a comment Login