Labaran Wasanni
Mesut Ozil: Ko Mikel Arteta zai sabonta kwantiragin dan wasan?
Yanzu haka dai kwantiragin Ozil a Arsenal zai kare ne a watan farkon na kakar wasa mai zuwa ta 2021.
Rashin tabuka abin a zo a gani da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ke fama dashi a wannan lokacin, ya sanya alamar tambaya ga matakin da Mikel Arteta ya dauka na cigaba da ajiye dan wasa Mesut Ozil a kan benci.
Tun dai a watan Maris da Arsenal ta yi nasara da ci 1 da nema kan West Ham United, rabon da Ozil ya taka wasa a kungiyar.
Arteta ya dauki matakin cire dan wasan daga tawagar ‘yan wasa 25 da zasu fafata a gasar firimiya da kuma Europa League a watan Oktoba da ya gabata.
Ozil dai ya ce, ko kadan bashi da aniyar barin kungiyar har sai lokacin da kwantiragin sa ya kare a karshen wannan kakar wasanni da muke ciki.
Arsenal tasha kungiya a wannan lokacin inda ta samu cin kwallo 10 a wasanni 11 kuma ta dawo mataki na 15 a kan tebirin gasar firimiya ta kasar Ingila.
Tsohon jami’in wucin gadi da ya rike Arsenal a shekarar 2019 bayan an kori Unai Emery, Freddie Ljungberg ya saka Ozil a cikin nagartattun ‘yan wasa 4 a kungiyar da sukafi kowa kokari a gasar firimiya ta Ingila a kakar wasa data gabata.
You must be logged in to post a comment Login