Labaran Wasanni
Mikel Arteta ya sabunta kwantaraginsa da Arsenal
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya sabunta kwantaragin shekaru uku da tawagar da ke birnin London.
Dan kasar Spain Mikel Arteta sabon kwantaraginsa da kungiyar zai kaishi har zuwa shekarar 2025 a filin wasa na Emirates.
Mai shekara 40 ya dai fara jagorantar tawagar birnin London a watan Disambar 2019 bayan sallamar Unai Emery.
Dan kasar Spain dai tuni ya fara yunkurin kai tawagar gasar cin kofin zakarun turai bayan tsawon shekaru biyar da suka shafe ba su je ba.
Yanzu haka dai Arsenal na mataki na hudu da maki 63 a wasanni 34 da wasanni kadan ya rage a kamalla kakar wasannin shekarar 2021/2022.
You must be logged in to post a comment Login