Coronavirus
Ministan lafiya ya ce cutar corona ta yadu a kananan hukumomi 586
Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ya ce cutar corona ta yadu a kananan hukumomi 586 cikin kananan hukumumomi 774 da ke fadin kasar nan.
Dr Osagie Ehanire na bayyana hakan ne a jiya, jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartaswa ta kasa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Ministan ya bayyana damuwarsa kan yadda kawo yanzu cutar corona ke ci gaba da yaduwa tare da tabarbare harkokin tattalin arzikin kasar.
Ehanire ya kuma bayyana cewa, majalisar zartaswa ta amince da a kashe sama da naira biliyan takwas don sayan wasu kayayyaki guda 12 a hukumar NCDC don yaki da cutar, wadanda za a raba a cibiyoyin da ke gwajin cutar don bunkasa ayyukan su.
Ta cikin jawabin nasa, Ehanire, ya ce a yanzu haka wadanda suka kamu da cutar a kasar nan sun kai dubu 47, 290 yayin da mutuane dubu 33, 609 suka warke, sai kuma wadanda suka rasu su 956 cikin jihohi 36 kamar yadda NCDC ta tattara alkaluman.
You must be logged in to post a comment Login