ilimi
Mun ƙara wa’adin rijistar ɗalibai- BUK

Jami’ar Bayero ta ƙara tsawaita wa’adin yin rijistar dalibai.
Jami’ar ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai Lamara Garba Azare ya fitar a yammacin Litinin.
Sanarwar ta ce, za a rufe yin rijistar a ranar 30 ga watan Satumbar 2023, kuma ba za a sake tsawaita wa’adin ba.
Har ma ya ce, bayan zama da hukumomin gudanarwar jami’ar suka yi, sun yanke hukuncin a ƙara wa’adin sakamakon kiraye kirayen buƙatar hakan.
Rahoton: Madina Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login