Labarai
Mun gano ƴan kwangilar layin dogo na yin aiki da karfe mara inganci Minista
Gwamnatin tarayya, ta bayyana matsalar rashin rashin tsaro a matsayin dalilin da ya sanya ba za ta faɗi wa’adin kammala aikin layin dogon da ya tashi daga Kano zuwa Kaduna ba.
Ministan sufuri Alhaji Sa’idu Ahmad Alƙalin, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke duba aikin da kuma yadda za a kammala aikin a kan lokaci domin sauƙaƙa harka sufuri.
Ministan ya ce, yanzu haka gwamnati za ta mayar da hankali wajen ganin an kammala aikin cikin gaggawa, sai dai rashin tsaro ya sanya dole a riƙa bi a hankali da kuma samar da ingantattun kayan ayyukan da ake aiki da su.
Haka kuma ya ce, yanzu haka ya gano wani ƙarfe da ƴan kwangilar ke yin aiki da shi a kan titin layin dogon wanda ba shi da inganci kuma baida inganci kuma ɓata gari za su iya zuwa su kwance shi, don haka ya umarci ƴan kwangilar da su gaggauta canja shi su saka wanda ba za a iya cirewa ba bayan an kammala aikin.
Ministan sifurin ya ce, wannan aikin zai kasance an kammala shi da wuri kasancewar layin dogon zai wuce ne har zuwa birnin Maraɗi na jamhuriyar Nijar.
You must be logged in to post a comment Login