Labarai
Mun kammala shirin fara bada tallafin Naira dubu 20 ga matasan Najeriya – MD SPW
Shugaban kwamitin shirin bada tallafin Gwamnatin tarayya na Naira dubu ashirin-ashirin duk wata da aka fi sa ni da (SPW) a nan jihar Kano, Farfesa Mukhtar Muhammad Dauda, ya ce shirin ya cimma nasara da ya kamata kasancewar kwamitin ya kammala tattara bayanan mutanen da za su ci gajiyar shirin a fadin Kano.
Farfesa Mukhtar Muhammad Dauda na Jami’ar Bayero ta Kano da aka fi sani da Farfesa MD Mukhtar, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da wakilin Freedom Radio Umar Idris Shuaibu, bayan cikar wa’adin aikin da suka fara gudanarwa sama da kwanaki 86 da suka gabata.
Ya ce, ya na da matukar kyau mutane su kwana da sanin cewa, bata gari na nan na yawo don damfarar mutane da sunan za su shigar da su cikin tsarin don amfana daga tallafin.
Ya kara da cewa tuni wakilan al’umma a sassan jihar Kano suka tattarowa wannan kwamiti mutanen da suke ganin sun cancanci samun wannan tallafin a yankuna su, ta hanyar basu fam su cike bayanan su.
“ya ce, duk wanda bai bi hanyar da ya kamata ba, ka da wani da baya kishin kasa yazo da wasu dabaru daban ta hanyar karbar kudaden jama’a don sanya su cikin wannan tsari domin tuni wannan kwamiti na mu ya kammala tattara bayanan sa, ya kuma aike da sunayen ma’aikatar ayyuka ta tarayya karkashin karamin minista Festus Keyamo.”
Shugaban kwamitin bada tallafin Naira dubu ashirin-ashirin na Gwamnatin tarayyar anan Kano ya ce manufar shirin shi ne don bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma rage radadin da annobar COVID-19 ta yiwa jama’a.
Farfesa Mukhtar Muhammad Dauda ya kuma kara da cewa, tuni suka tattara rahotanni kan ayyukan da bangarorin jihar nan ke bukata na raya kasa, don don cin gajiyar dimbin al’ummar jihar Kano a yankuna daban-daban.
Tun da fari dai an kaddamar da kwamitin nemo mutane 1000 a kowacce karamar hukuma don cin gajiyar wannan tallafi na Naira dubu ashirin-ashirin ne a ranar 28 ga watan Yunin bana, inda shugaban kwamitin na jihar Kano Farfesa Mukhtar Muhammad Dauda ke cewa nan bada dadewa wadanda aka zabo za su fara karbar tallafin nasu don bunkasa rayuwar su.
You must be logged in to post a comment Login