Kiwon Lafiya
Mun samar da cibiyoyin lafiya sama da 1000 a Kano – Ganduje
Gwamnatin jihar kano ta ce, ta samar da cibiyoyi kula da lafiya a matakin farko sama da dubu daya musamman a yankin karkara don samar da ingantacciyar lafiya ga al’ummar jihar.
Babban sakatare a hukumar lafiya matakin farko Dakta Tijjani Hussain ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin ”Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom.
“Muna kulawa da asibitocin da suke yankunan karkara domin samarwa da al’umma cikakkiyar lafiya, sakamakon yadda ake yawan samun matsaloli a asibitocin karkara musamman na rashin zuwan ma’aikata aiki da kuma cin zarafin marasa lafiya” inji Dakta Tijjani
Ya ce, tuni aka samar da ma’aikatan lafiya sam a da dubu tara a cibiyoyin, da aka samar don tabbatar da an bai wa al’umma kulawar da ta dace.
“Mun dauki matakin fara tantance ma’aikatan da suke yin aiki a cibiyoyin lafiya a fadin jihar Kano, donzagulo na bogi da marasa kwarewar aiki da masu aikata laifukan da suka sabawa dokar aiki” a cewar Dakta Tijjani.
Babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko ta jihar kano kenan Dakta Tijjani Hussain da ya kasance ta cikin ”Barka da Hantsi na tashar Freedom.
You must be logged in to post a comment Login