Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna bukatar sanin inda Dadiyata ya ke-Kungiyoyi

Published

on

Kungiyar mai rajin kare Demokaradiyya, wato UFDD, da hadakar kungiyoyin kishin al’umma sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna, da sauran jami’an tsaro da su bayyanawa al’ummar kasar nan halin da matashi dan gwagwarmaya a kafofin sada zumunta Abubakar Idris Dadiyata, yake ciki kimanin kwana, 82 bayan da aka dauke shi har cikin gidan sa a jihar Kaduna.

Hadakar kungiyoyin ,sunyi kiran ne a yau a wani taron manema labarai da suka kira ,don bayyana matsayar su da kuma sanin halin da yake ciki.

Da yake jawabi a madadin  hadakar kungiyoyin Isma’il Auwal, yace abun takaici ne matuka a ce a lokacin mulkin demokradiyya, kuma a gwamnatin da take rajin samar da zaman lafiya da tsaro, a ce dan kasarta ya yi batan dabo da har yanzu iyalin sa ,da iyayen sa basu san halin da yake ciki ba har zuwa yanzu.

Haka kuma kungiyoyin sun nemi da a jami’an tsaro da su yi cikakken bayani akan abinda suke da masaniya akan Dadiyata, duba da cewar su a kungiyance basu gamsu da yadda nemo matashin malamin jami’ar yake gudana ba a yanzu haka.

Wakilinnu Aminu Halilu Tudun Wada, ya ruwaito mana cewa hadakar kungiyoyin sun sha alwashin yin zanga zangar lumana da kuma yin zaman dirshan a ofisoshin jami’an tsaro da lamarin ya shafa don nuna damuwar su matukar ba a dau matakin da ya kamata ba na kubutar da matashin dan gwagwarmayar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!