Connect with us

Labarai

Rufe mashigar Hormuz na dakile tattalin arzikin duniya- Antonio Guterres

Published

on

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce rufe mashigar Hormuz na taɗiye tattalin arzikin duniya.

 

Antonio Guterres  ya bukaci a gaggauta buɗe masigar Hormuz, a bada dama ga dukkanin jiragen ruwa su wuce, a bar tattalin arzikin duniya ya numfasa.

 

Ya ce ko a yanzu aka janye takunkumin, harkar samar da kayayyaki za ta dauki watanni kafin ta farfado, lamarin da zai haifar da raguwar samar da kayayyaki da kuma tashin farashi.

 

Ya bayyana hakan ne yayin da dakarun juyin juya halin Iran sukai gargadi cewa, za su kaddamar da zafafan hare-hare masu dogon zango kan Amurka, idan Washington ta sake kai wa Iran hari.

 

Tun bayan da rahotannin suka ce Shugaba Donald Trump na samun bayanai kan yiwuwar ɗaukar matakin soja a kan Iran, farashin ɗanyan mai yayi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!