Labarai
Muna neman gwamnati ta sake duba batun rufe makarantu – Kwamaret Ayagi
Kungiyar da ke fafutukar kwato hakkin dan Adam ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi duba kan sha’anin bude makarantu a kasar nan wanda annobar corona ta tilsata rufewa tsawon watanni.
Hakan na cikin sanarwar da daraktan kungiyar Kwamared A.A Haruna Ayagi ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta Human Right Network ta lura da yadda rufe makarantu ke kara ta’azzara laifukan cin zarafi a kasar nan, tare da barazanar tabarbarewar ilimi musamman ga daliban firamari.
Sanarwar ta kara da cewa, kamata ya yi ministan ilimi Adamu Adamu ya kara nazartar yadda za a bude makarantun kasar nan kamar yadda a baya bayan nan a bude guraren gudanar da al’amuran yau da kullum na cakuduwar jama’a.
Ka zalika kungiyar ta yi kira da a kara nazartar yiwuwar bai wa daliban da ke shirin kammala babbar sakandire damar rubuta jarrabawar WAEC da takwarorin su na karamar sakandire har ma da daliban firamare da ke shirin rubuta jarrabawar shiga karamar sakandire.
You must be logged in to post a comment Login