Labaran Kano
Musulmai su dinga aikata ayyukan alheri – Empathy Foundation
Gidauniyar tausayawa da tallafawa mabukata wato Empathy Foundation ta ja hankalin al’ummar musulmi da su zage dantse wajen aikata ayyukan alkheri a wadannan kwanaki goma da muke ciki na zulhijja.
Shugaban kungiyar Mansur Musa Gabari ne ya bayyana hakan yayin da gidauniyar ta ziyarci gidan yara masu lalurar kwakwalwa ta ‘Torrey home’ dake unguwar Tudun Maliki da gidan kangararrun yara na Goron Dutse wato ‘Remand home’ da na masu lalurar yoyon fitsari don raba musu kayan abinci.
Mansur Musa Gabari ya kuma ce, yana da kyau masu wadata su rika tallafawa wadanda basu dashi musamman a lokutan salla.
Tun farko da take jawabi, shugabar gidan kula da yara masu lalurar kwakwalwa ta ‘Torrey home’ da ke unguwar Tudun-Maliki, Lauriya Sagir Garba, ta yabawa Gidauniyar ta Emphaty tare da bukatar masu hannu da shuni
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa, a yau gidauniyar ta Emphaty za ta ziyarci Dawakin Kudu don bayar da tallafin kwanan rufi ga wani masallaci da ruwan sama ya yaye rufinsa.
You must be logged in to post a comment Login