Ƙetare
Mutane 14 sun mutu a Kamaru sakamakon hatsarin mota
Akalla mutane 14 ne suka mutu a kasar Kamaru sakamakon wani mummunar hatsarin da wata mota kirar Bus ta yi a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wata sanarwa da Ministan sifurin kasar Jean Ernest Massena Ngalle Bibehe ya fitar, ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne ranar Talata a kauyen Lom da ke yankin Adamaoua, inda ya ce, wani yaro mai shekara 10 na daga cikin wadanda suka mutu.
Wata majiya a wani asibiti da ke kusa da Garoua-Boulai ta ce, mutane 68 ne suka jikkata a hatsarin.
Tun a baya dai, alkaluman Hukumar lafiya ta Duniya sun nuna cewa kasar Kamaru na daya daga cikin kasashen Afirka da ke kan gaba wajen samun yawaitanrmace-mace a haduran mota.
Ko a shekarar 2018, kasar ta samu mutuwar sama da mutane 7,000 a haduran ababen hawa.
You must be logged in to post a comment Login