Labarai
Mutane 18 sun rasu sanadiyyar hatsarin kwale-kwale
A kalla mutane 18 ne suka rasa rayuwakansu sakamakon hatsarin kwale-kwale a Kogin Buji da ke karamar hukumar Itas Gadau.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar ta su,ta cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar DSP Ahmed Muhammed Wakil ya fitar, ta ce 16 daga cikin wadanda suka rasa rayukansu kananan yara ne.
Sai dai yace, masu aikin ceto sun samu nasarar ceto mutane biyar wadanda biyu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan jirgin kwale-kwalen yana dauke ne da manoma ashirin da uku lokacin da ya yi hatsarin.
Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da: Abdulraham Shehu; Suwaiba Yusuf, Saude Abdulkarim, Fatima Maigari, Zuwaira Maigari, Hari Maigari, Hussaina Maigari, Ummani Abdulkarim da kuma Halima Saminu.
Sauran sune: Najaatu Hamza, Nura Abdullahi, Yahuza Abdullahi, Hafsa Abdullahi, Sadiya Hashimu, Khadija Alhassan, Amina Idris, Kaltime Hudu da kuma Furaira Malam Magaji.
You must be logged in to post a comment Login