Connect with us

Labarai

Mutane 44 sun rasu sakamakon barkewar cutar Mashako a Zamfara

Published

on

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Zamfara ta ce mutane 44 sun mutu sakamakon barkewar cutar Diphtheria a wasu sassan jihar.

Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a na ma’aikatar, Dakta Yusuf Haske, ne ya bayyana hakan da cewa zuwa yanzu an samu mutane 367 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da sama da 320 daga cikinsu aka yi wa magani tare da sallamarsu.

Ya ce gwaje-gwajen da aka gudanar kan wadanda ake zargin sun kamu da cutar sun tabbatar da kasancewar kwayar cutar ta Diphtheria watau mashako.

Dakta Yusuf Haske, ya ce, bayan tabbatar da barkewar cutar, gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta tura kungiyoyin gaggawa zuwa kananan hukumomi 14 na jihar domin wayar da kan mutane kan yadda za su kula da kansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!