Kowane Gauta
Na amince ayi sulhu tsakanina da Kwankwaso – Ambasada Aminu Wali
Guda daga cikin jagororin jam’iyyar PDP a jihar Kano Ambasada Aminu Wali ya ce, ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso jagoran darikar kwankwasiyya amma bisa sharadi.
Ambasada Aminu Wali yace daga cikin sharadin shine dole ne abi doran tsarin mulkin jam’iyyar PDP wanda jama’ar da aka samu abasu damar zabar wadanda suke so amma ba shugaban jam’iyya ko wani ya yi musu kutse ba wajen dagewa kan wanda zasu zaba.
Aminu Wali ya bayyana hakan ne a cikin shirin kowanne Gauta na tashar Freedom Radiyo dake nan ta cikin shirin Kowanne Gauta.
Aminu Wali yace matukar jama’a suna sanka kuma sun zabeka ko ba kada ko sisi dole ayi da kai domin hakan shine Demokradiyya.
You must be logged in to post a comment Login