Addini
NAHCON da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar Alhazai sun sanya hannu
Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya NAHCON, ta tabbatar da cewa, yaƙin da ake yi a Sudan zai shafi jigilar mahajjatan Nijeriya na bana, don haka za a bukaci karin kudade daga maniyyatan.
Hukumar ta tabbatar da hakan ne da yammacin Talatar makon nan bayan da hukumar da kuma kamfanonin sufurin jiragen sama na cikin gida suka sanya hannun kan yarjejeniyar jigilar maniyyatan na bana.
A baya dai hukumar da kamfanonin sun gaza cimma hakan matsaya kan wannan batu a makon jiya saboda batun karin kudin.
A cewar Kwamishinan kula da tsare-tsare da gudanar da aikin Hajji a hukumar ta NAHCON, Abdullahi Magaji Hardawa, kamfanonin sifurin jiragen saman sun nemi sai an daddale da su kafin sanya hannu a kan yarjejeniyar.
You must be logged in to post a comment Login