Connect with us

Labarai

Yan tada ƙayar bayan fafutukar ɓallewa a Kamaru sun ayyana dokar kulle

Published

on

Mayaƙa masu fafutukar ɓallewa a kasar Kamaru sun ayyana dokar kulle na tsawon mako guda a yankunan biyu na ƙasar da ake amfani da harshen Ingilishi.

 

Matakin ya haifar da tsaiko yayin da ake fara sabuwar shekarar karatu, tare da taƙaita zirga-zirga a yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma.

 

A birnin Buea da ke yankin Kudu maso Yamma, jami’an tsaro sun bazu a kan tituna, yayin da suke gudanar da bincike gida-gida.

 

An kashe kimanin mutum 6,000 a rikicin da ya kwashe shekara 10 tsakanin gwamnatin Kamaru mai amfani da harshen Faransanci da ƴan aware masu magana da Ingilishi, waɗanda ke fafutukar kafa ƙasa mai cin gashin kanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!