Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Nasir El Rufa’i ya dakatar da zuwa Masallaci da Majami’U

Published

on

A yunkurin gwamnati na takaita barazanar yaduwar cutar Corona virus, cikin al’ummar ta , gwamnatin jihar Kaduna, ta hana tare da takaita taruwar mutane da yawa a waje daya, ciki har da Sallar Jumma’a da taron Coci -Coci na ranar Lahadi , ga dumbin al’ummar Musulmai da Kiristoci.

A wata takarda data fito daga fadar gwamnatin jihar a yau, mai dauke da da suna da sa hannun Muyiwa Adekeye, mai baiwa gwamnan jihar ta Kaduna shawara a kafafen yada labarai, ta umarci limamai da kada su jagoranci Sallar Jumma’a tare da koyi da gwamnatin kasar Saudia da tayi hani da hakan , a matsayin ta na jagorar Addinin Musulunci a yunkurin da ake na takaita yaduwar cutar a manyan Masallatan Makka da Madina.

Sanarwar ta kara dacewa, kasashe da dama na musulmai da suka hada da ,Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, Kuwait, Saudi Arabia, sun umarci al’umma da su gudanar da ibadar su a gida , tare da takaita zirga zirga cikin cunkoso, don haka gwamnatin jihar Kaduna, ta umarci a dena salloli biyar na rana a cikin al’umma har sai an shawo kan wannan annoba ta Corona mai taken Covid 19.

Sanarwar ta kuma ce, in har kasashe masu yawan Kiristoci kamar Italia, France da Germany zasu hana zuwa Coci, mai zai hana koyi dasu ,don haka muna kira da Limaman Coci-coci , da makaman tansu dasu dau matakan rage cunkoson al’umma, tare da takaita haduwar al’ummar da ba zata gaza ko haura sama da mutum 10 ba.Don haka duk wani taro da ya haura mutum sama da 50, an haramta shi nan take har zuwa wani takaitaccen lokaci.

Bugu da kari sanarwar , ta tabbatar da rufe dukkanin ilahirin makarantun jihar, kama daga kan kananan Makarantu na Nursery, Firmare, Sakandire, da manyan makarantu da zai fara aiki nan take , tun daga ranar Litinin din mako mai kamawa ta 23 ga watan Maris, tare da rufe Jami’ar Kaduna, Kwalejin Nuhu Bamalli, Kwalejin Ilimi da koyon aikin unguwar Zoma, har nan da tsawon wata daya, kafin ganin halin da ake ciki.

Haka kuma, an hana taruwa nan take a wajen, shakatawa na gidajen rawa, cin abinci, mashaya, da tashoshin motoci , tare da taron shakawata na yin raye -raye, har zuwa abinda hali ya yiwu.

Don haka, gwamnatin tayi kira ga al’umma, shugabannin addinai, dana al’umma, dasu yi iya bakin kokarin su wajen taimakawa gwamnatin a yunkurin da take na kare lafiyar al’ummar ta.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!