Labarai
Neman Haƙƙi: Kano Pillars ta nemi kamfanin Aiteo ya biya ta miliyoyin kuɗaɗe
Kano Pillars ta nemi kamfanin Aiteo da ya biya ta haƙƙoƙinta na kuɗi har miliyan 25 na lashe gasar kofin ƙalubale ta ƙasa a shekarar 2019.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Surajo Yahaya Janbul ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawa da manema Labarai.
Janbul ya bayyana ƙalubalen da ƙungiyar ke fuskanta a kakar wasannin bana.
A cewar sa, ƙungiyar na fama da rashin kuɗaɗen gudanarwa, da matsalar motar zirga-zirga zuwa wasanni da kuma rashin tsayayyiyar shalkwata ta din-din-din.
Alhaji Janbul ya nanata cewa, “Muna kira ga mahukuntan shirya Firimiya ta ƙasa, da hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa NFF da duk masu ruwa da tsaki, kan su saka baki a gaggauta biyan mu kuɗaɗen Aiteo Cup da muka ɗauka na Naira miliyan ashirin da biyar”.
Ya ƙara da cewa, samun wannan kuɗi zai taimaka wa ƙungiyar wajen gudanar da harkokinta musamman na gasar Firimiya ta ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login