Labarai
NERC ta fayyace yadda farashin lantarki zai kasance
Hukumar kula da bangaren samar da wutar lantarki ta kasa NERC ta kara fayyace yadda farashin lantarki zai kasance.
Hukumar ta NERC ta ce karin kudin wuta da aka yi a baya-bayan nan bai shafi muaten da ke samun wuta kasa da awanni goma sha biyu a duk rana ba.
Kwamishina mai kula da harkokin shari’a da ba da lasisi na hukumar Mista Dafe Akpeneye ne ya fayyace hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a kafar internet.
A cewar sa, dukkannin abokin huldar kamfanonin rarraba wutar lantarki da basa samun wuta akalla awanni goma sha biyu a rana to basa cikin karin farashin da aka yi.
A ranar daya ga wannan wata na Satumba ne kamfanonin rarraba wutar lantarki suka sanar da sabon tsarin farashin wutar lantarki.
You must be logged in to post a comment Login