Connect with us

Labaran Wasanni

Newcastle United ta dauki Callum Wilson daga Bournemouth

Published

on

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, Callum Wilson, ya rattaba hannu a sabon kwantiragin shekara 4 da kungiyar Newcastle United kan kudi Yuro miliyan 20.

Wilson, mai shekaru 28, ya yi nasarar jefa wa Bournemouth kwallaye 67 a wasanni 187 da ya taka leda a kungiyar.

Dan wasan dan asalin kasar Ingila, ya ce, ya amince da komawa Newcastle United kai tsaye a dai-dai lokacin da ya samu labarin kungiyar na son daukar shi.

Da farko dai Aston Villa ta fara zawarcin dan wasan kafin daga baya ta janye batun, duba da Wilson yafi kaunar komawa Newcastle United.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,994 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!