Labarai
NFF: Ta musunta zaben Amaju Pinnick a matsayin mataimaki na 5 ga shugaban CAF
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta musunta jita-jitar da ke cewa an zabi shugaban hukumar Amaju Pinnick a matsayin mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF na biyar da aka gudanar a birnin Rabat da ke kasar Morocco.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren hukumar ta NFF Dakta Mohammed Sanusi ya fitar, inda ya ce ko kadan ba a tattaunawa wannan batu da NFF ko CAF ba.
“An dai zabi Amaju Pinnick ne a matsayin Mamba a Majalisar Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a zaman majalisar na 43 da aka gudanar a ranar Juma’a 12 ga watan Maris,” inji Dakta Sanusi.
Haka zalika, CAF ta gudanar da taron kwamitin zartarwa na farko a ranar Asabar bayan da Patrice Motsepe ya zamo shugaban hukumar.
A wata nasarwa da CAF ta wallafa a shafinta ta bayyana Augustin Senghor a matsayin mataimaki na daya sai Ahmed Yahya mataimaki na biyu sai Suleiman Waberi mataimaki na uku sai kuma Kanizat Ibrahim mataimaki na biyar yayin da Veron Mosengo-Omba ya zamo babban sakataren hukumar.
You must be logged in to post a comment Login