Labaran Wasanni
NFF ta nada sabon mai horar da kungiyar Super Eagles
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta nada Jose Peseiro a matsayin sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles.
Hukumar ta NFF ta sanar da hakan ne a ranar Laraba 29 ga watan Disambar shekarar da muke ciki ta 2021.
Jose Peseiro shine zai maye gurbin tsohon mai horar da tawar ta Super Eagles Gernot Rohr da aka sallama bayan da ya shafe shekaru biyar yana jagorantar ta.
Kafin nadin nasa Najeriya dai ta nada tsohon dan wasan kasar Augustine Eguavoen a matsayin mai horarwa na rikon kwarya.
Augustine Eguavoen da kawo yanzu tuni ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 28 da za su wakilci Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafar Afrika da za a gudanar a kasar Kamaru a shekara ta 2022 mai kamawa.
Zuwa yanzu ana saran sabon mai horar da kungiyar Jose zai fara shirin tin karar gasar ta AFCON da za ta fara gudana daga ranar 9 ga watan Janairun 2021.
Sabon mai horarwar dan kasar Portugal ya kuma yi fatan kai Najeriya zuwa gasar cin kofin Duniya da za a gudanar a kasar Qatar a shekara ta 2022.
You must be logged in to post a comment Login