Ƙetare
Nijeriya ta katsewa Nijer wutar lantarki
Najeriya ta dauki matakin katse layin wutar lantarkin da yake kaiwa kasar Nijar wuta, biyo bayan takunkumin da aka kakaba wa gwamnatin mulkin sojan kasar da ta hambarar da zababben shugaban kasar.
Wata majiya daga kamfanin samar da wutar lantarki ta Niger Nigelec ta bayyana cewa, “Tun a jiya, Najeriya ta katse layin wutar lantarki da ke jigilar wutar lantarki zuwa Nijar.”
Nijar dai ta dogara ne da Najeriya wajen samun wutar lantarki da akalla kashi 70 cikin 100, inda ta siya daga kamfanin Mainstream na Najeriya, a cewar Nigelec, wanda shi ne ke samar da wutar lantarki a kasar.
Domin samun wutar lantarkinta kasar Nijar na kokarin gina madatsar ruwa ta Kandadji a kogin Neja, mai tazarar kilomita 180 (mil 110) daga Yamai.
Ana sa ran kammala aikin dam din a shekarar 2025 kuma ana sa ran samun wutar lantarki mai karfin migawatt 629 a shekara (GWh).
Firayim Minista Ouhoumoudou Mahamadou ya bayyana damuwarsa game da tasirin takunkumin, yana mai cewa, “Takunkumin zai yi wa kasarmu illa sosai,” a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta Faransa ta France 24.
You must be logged in to post a comment Login