Labaran Wasanni
Principal Cup: Zai magance dogaro ga masu taka leda a ketare
Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce matukar aka farfado da gasar cin kofin makarantun sakandire a fadin kasar nan, to ba sai an dogara ga ‘yan wasan Najeriya dake taka leda a kasashen waje ba.
Sunday Dare ya bayyana haka ne a jihar Lagos, yayin taron gabatar da hoton gasar da kuma jagororin da za’a yi amfani da su wajen gudanar da gasar ta wannan shekarar da muke ciki.
Ministan ya ce, “A matsayin sa na minista ya taba shawartar shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa Amaju Pinnick da ya taka zuwa kasar Ingila don ya roki dan wasa Bukayo Saka ya bugawa Najeriya wasa”.
Ya kuma ce, idan aka inganta tare da farfado da gasar cin kofin makarantun sakandire tun daga matakin farko, babu bukatar tada jijiyar wuya wajen lallashin wani dan wasa don shigawa tawagar kasar nan.
A nasa bangaren shugaban hukumar NFF Amaju Pinncik, ya ce, “NFF ta shirya tsaf wajen bada duk irin gudunmowar da masu shirya gasar ka iya bukata a ko da yaushe”.
You must be logged in to post a comment Login