Rahotonni
Rahoto: Likitoci a Kano sun tsindima yajin aiki
A safiyar yau Litinin ne gamayyar kungiyoyin likitoci ta kasa wato National Association of Resident Doctors (ARD) ta tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani saboda zargin gwamnatin tarayya da kin biyansu wasu hakkoki su da kuma rashin samar da kayan kariyar kamuwa daga cutar corona da biyansu alawus-alawus din su na wasu mambobinsu da aka sallama daga bakin aiki da sauran bukatun.
Wasu marasa lafiya da Freedom Radiyo ta zanta da su a asibitin Aminu Kano lokacin data iske su da misalign karfe 12 rana suna jiran zuwan likita don duba lafiyarsu, sun ce har zuwa wannan lokaci likitocin ba su zo ba.
Sun kuma ce tun da sanyin safiya suka zo asibitin har zuwa wannan lokaci basuga likitaba, sai dai wasu daga cikin ma’aikatan Asibitin sun shaida musu cewar wasu daga cikin likitocin sun tafi yajin aiki a yau wanda hakan ne yasa babu likitocin daya kamata.
Gwamnatin Kano za ta rage kasafin kudin 2020
Abinda ya sa likitoci suka shiga yajin aiki a Najeriya
Wasu mutane da suka kawo marasa lafiya asibitin sun shaidawa Freedom Rediyo cewa an samu cikowar marasa lafiya a asibitin yau amma kuma babu wadatattun likitocin da za su duba marasa lafiya.
Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta biyawa likitocin bukatun nasu ko sa dawo bakin aikin duba da irin muhimmancin aikinsu ga jama’a musamman a wannan lokaci na cutar corona.
Shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewar reshen asibitin Aminu Kano, Dakta Abubakar Nagoma Usman, ya bayyana dalilan da suka sanya suka tsunduma yajin aikin na yau.
Ya ce duba da yadda jama’a ke matukar bukatar ayyukan nasu musamman a wannan lokacin ya sanya kungiyar ta sahalewa wasu daga cikin mambobinta da ke aiki a bangaren da ake lura da wadanda suka kamu da cutar corona na dan lokaci.
Sai dai yace ma’aikatan su dake aiki a bangaren da aka killace mutanan da suka kamu da Corona zasu ci gaba da ayyukan su a wajen nadan lokaci, wanda idan aka kasa samun dai-daito da gwamnatin ta tarayya suma zasubi takwarorin su wajen tsunduma yajin aikin.
Dakta Abubakar Nagoma ya kara da cewa tun daga shekarar 2017 kungiyar tasu ke godon gwamnati ta biya musu bukatun nasu amma har yanzu ta ki ta biya, shin ya sanya suka tsunduma wannan yajin aiki na yau.
You must be logged in to post a comment Login