Manyan Labarai
Rahoto: Yawaitar makamai a hannun jama’a na kara janyo tabarbarewar tsaro a Najeriya
Yaduwar makamai a hannun mutanen da ba jami’an tsaro ba a Najeriya na ci gaba da karuwa, lamarin ya kara janyo tabarbarewar harkokin tsaro a kasar nan.
Matsalolin sun hadar da satar mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa, hare-haren ‘yan Boko Haram da ma ‘yan bindiga da kuma makamantansu.
Mallakar bindiga ba tare da izini ba babban laifi ne a Najeriya, wanda yanzu ake ganin yadda bata-gari ke mallakar makaman suna kashe jama’a ba gaira ba dalili.
Wasu lokutan ma da rana tsaka ake ganin ‘yan Boko Haram da ‘yan bndiga da sauran bata-gari suna aikata miyagun laifukan ba tare da wani tsoro ba, inda suke harbe-harbe suna sace mutane suna kuma kona wurare.
Mustapha Isyaku mai fashin baki kan harkokin tsaro, ya ce, rashin cikakken tsaro a kan iyakokin kasar nan na taimakawa wajen safarar makamai.
“Ko a baya-bayan nan rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kwance wani bam da aka ajiye a wata gona, sannan kuma ta samu nasarar kama wani mutum da ke safarar babura ga ‘yan bindiga a Jihar Zamfara,” a cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.
Abdullahi Haruna kiyawa ya yi kira ga jama’a da surinka baiwa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayyana rahoton duk wani abu da ba su amince da shi ba domin gudanar da bincike a kai.
You must be logged in to post a comment Login