Labarai
Rashin gaskiya ne ke kawo mace-macen aure – Masani
Wani masanin halayyar dan adam a jami’ar Bayero da ke nan Kano, ya bayyana cewar babban abinda ke haifar da mutuwar aure a kasar nan shi ne rashin gina auran akan gaskiya tare da rashin amana da kuma watsi da al’dun malam bahaushe da aka yi.
Farfesa Baffa Aliyu Umar, Malami a sashen nazarin halayyar dan Adam da zamantakewa a Jami’ar Bayero dake nan Kano, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan tashar freedom rediyo wanda aka tattauna a kan matasalar yawaitar mutuwar aure a kasar nan.
Baffa Aliyu Umar ya kuma ce, matukar za a ci gaba da gudanar da sha’anin aure kan son zuciya shakka babu lamarin aure zai ci gaba da tabarbarewa.
A nasa bangaren wani mai sharhin kan al’amuran yau da kullum, Malam Mustapha Adamu Indabawa, ya bayyana cewar matsalar na kara yawaita ne sanadiyyar rashin bincike da iyaye ke yi kafin aurar da yaransu.
Dukkannin bakin sun kuma ce kamata yayi iyaye su rika tunatar da ‘ya’yansu cewar aure bautane na ubangiji.
You must be logged in to post a comment Login