Labaran Kano
Rashin kwararrun masu karbar haihuwa ke janyo mutuwar jarirai- Likita
Wata kwararriyar likita a bangaren yara dake asibitin Malam Aminu kano, dakta Zubaida Farouk Ladan, ta bayyana cewa rashin samun kwararrun masu Karbar haihuwa na daga cikin ababen dake janyo mutuwar jarirai a kasar.
Dakta Zubaida Farouk ta bayyana hakane jim kadan bayan kammala Shirin barka da hantsi na Nan gidan radio freedom Wanda ya maida hankali kan irin cutukan dake addabar kananan yara a lokacin sanyi.
Ta Kara da cewa kaso mafi yawa na mutuwar jarirai yafi kamari ne a nahiyar afurka Wanda kuma Najeriya itace a Kan gaba inda jarirai dari biyar ne ke mutuwa a kowa ce rana.
Ya kamata Yan Najeriya su dakatar da zuwa asibiti kasashen waje-Buhari
Abinda ke ciwa mutane tuwo a kwarya a asibitin AKTH Kano
Asibitin AKTH zai gudanar da jarabawar kwarewa ga likitoci fiye da dubu
A nasa bangaren tsohon daraktan gudanarwa na asibitin koyarwa na Usman Danfodiyo Farfesa Mu’utasim Ibrahim yace akwai cututtuka da dama dake kama kananan yara lokaci na sanyi wanda mafi aksari suna Kama yara ne sakamakon rashin kulawa da Kuma karancin rigakafi da wasu iyayen ke kin kai yara asibiti.
Farfesa Mu’utasim Ibrahim ya kuma ce nan bada jimawa ba kungiyar kwararrun likitocin kananan yara dake kasar nan zasuyi taro a nan Kano kan irin matsalolin da suka shafi kananan yara inda kuma yaja hankalin iyaye dasu rinka kulawa da yaran su tare da kaisu asibiti a duk lokacin da suka fuskanci wani bakon abu game da yaran.