Labarai
Ronaldinho ya shaki iskar ‘yanci
Bayan shafe kwanaki talatin da biyu a cikin Kurkuku , a kasar Paraguay tsohon gwarzon dan wasan duniya karo biyu dan kasar Brazil Ronaldinho, da dan uwansa Roberto de Assis , sun shaki iskar ‘yanci bayan da Alkali Gustavo Amarilla ya bada belin su akan kudi sama da Fam miliyan daya.
An dai kama tsohon dan wasan na Barcelona ne a farkon watan Maris, shi da dan uwan sa bisa zargin shiga kasar Paraguay da fasfon Bogi , sai dai bayar da belin nasu, yanzu an sake su tare da yi musu daurin talala a gida har zuwa lokacin da za’a kammala bincike.
Jim kadan bayan shigar su kasar ta Paraguay a baya, hukumomin kasar suka damke su bisa zargin fasfon, tare da tisa keyar su zuwa gidan kaso na Agrupacion Especializada , bayan kama su da akayi a wajen shakatawa na’ Resort Yacht and Golf Club Paraguay’.
Labarai masu alaka.
Hanyar da Diago Simeone ya bi wajen fitar da Liverpool a Champion
‘Yan wasa na bada gudunmowa don yakar Corona Virus
A lokacin da yana gidan Kason, hotuna daban -daban hade da bidiyon dan wasan sun yadu a shafukan sadarwa na Zamani, da yake Kwallo da aiyyukan nishadantar da jama’a a gidan kason.
Sai dai duk da haka, Ronaldinho da dan uwansa sun musanta aikata ba dai -dai ba , inda yace fasfon dan kasuwar kasar Brazil Wilmondes Sousa Liria, ne ya basu shi kyauta don haka basu da masaniyar cewar na bogi ne.
Sai dai a bayyane yake dan wasan bai ji dadin abinda ya faru ba ,kamar yadda tsohon dan wasan kasar Paraguay , Nelson Cuevas ya bayyana wa gidan Rediyon CNN, “Kowa ya san shi da nishadi da murmushi amma yanzu haka dana ke muku magana dana je gaisawa da duba Abokina murmushin sa yayi kaura sakamakon yana wajen da bai saba dashi ba “.
Tsohon dan wasan Paris Saint Germain, Barcelona da Ac Milan, Ronaldinho ya wakilci kasar sa ta Brazil har sau 97 inda yq zura Kwallo 33, daga shekarun 1999 zuwa 2013, yana kuma daga cikin jiga jigan ‘yan wasan da suka daukar wa kasar Kofin duniya na shekara ta 2002.
You must be logged in to post a comment Login