Labarai
Ronaldo zai yi ritaya daga kwallon kafa a karshen kakar wasanni ta bana

Ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa bayan kammala kakar wasannin shekarar 2026/2027.
Ronaldo mai shekaru 41 ya bayyana hakan ne a wata hira da mujallar Vogue a yau Lahadi.
Kyaftin ɗin na Portugal, kuma tsohon ɗan wasan Manchester United, Real Madrid da Juventus, wanda ya zura ƙwallaye sama da 950, ya ce tuni ya tsara yanda rayuwarsa zata kasance bayan yin ritaya, inda zai riƙa yin tafiye-tafiye da buga wasan Padel.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Ronaldo ya angwance da abokiyar zamansa, Georgina Rodriguez, a makon da ya gabata, bayan shafe kusan shekaru 10 suna tare, a wani bikin aure na musamman da aka gudanar a birnin Cascais na Portugal.
You must be logged in to post a comment Login